$Q Daga Ka’idar AI Zuwa Cikakken Tattalin Arziki: Yadda Quack AI Ke Haɗa Ginshiƙan Agent Economy.
Ginshiƙin tattalin arzikin AI yana ƙara kammala siffa a duniyar Web3. Fitowar fasahar ERC-8183 babban ci gaba ne domin ta kawo sabon commerce layer wanda zai baiwa AI agents damar karɓar aiki, tsara yarjejeniya, da kammala sakamako a kan-chain. Amma gaskiyar magana ita ce: tsarin kasuwanci kaɗai ba ya wadatar don cikakken tattalin arziki mai cin gashin kansa.
ERC-8183 na iya ayyana yadda aiki zai gudana, amma aiwatar da biyan kuɗi cikin sauƙi da tsaro yana buƙatar wani tsarin da ya fi ƙarfin hakan. A nan ne fasahar Q402 da tsarin Quack AI
@QTalk ke shiga tsakani.
Yayin da ERC-8183 ke bayyana aikin da yarjejeniya, Q402 yana ba da damar aiwatar da biyan kuɗi kai tsaye a kan-chain ba tare da buƙatar gas ba, kuma a ƙarƙashin tsauraran dokoki da aka riga aka gindaya. Wannan yana nufin AI agents za su iya gudanar da mu'amala cikin tsari, tsaro, da gaskiya.
Idan muka duba tsarin gaba ɗaya, za mu ga yadda abubuwa ke haɗuwa cikin cikakkiyar hanya:
ERC-8004 → Yana tabbatar da asalin agent (Identity)
ERC-8183 → Yana tsara kasuwanci da aiki (Commerce)
Q402 → Yana aiwatar da biyan kuɗi (Payments)
Quack AI → Tana kafa dokoki da tsarin gudanarwa (Governance)
Ba za a iya samun cikakken cin gashin kai na AI ba tare da tsarin da ke sa ido da kuma doka ba. A nan ne
@QTalk Quack AI ke zama ginshiƙin da ke tabbatar da cewa agents suna aiki cikin iyakokin da aka gindaya.
Fitowar ERC-8183 ta nuna ainihin inda makomar Agent Economy ta dosa. Kuma Quack AI ta riga ta gina hanyoyin da za su haɗa dukkan waɗannan sassa domin wannan makoma ta zama gaskiya a aikace.
#QuackAI #Q402 #ERC8183 $Q